Advertisement

Responsive Advertisement

Abinda Yasa Har Yanzu Bamu Kama Kowa Kan Karancin Naira Ba, EFCC


 Shugaban EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa, ya ce hukumarsa ta ɗan jira ne don kar ta ƙara dagula tsarin sauya naira 

An yi tsammanin EFCC zata sa ido kan masu maida tsohon kuɗi bankuna domin cafke masu boye dammai a gida 

Bawa ya ce sabbin naira suna da lambobin da za'a iya gano daga inda suka fito kuma me aka yi da su 

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon kasa (EFCC) ta ce ba ta maida hankali wajen kama waɗanda ake zargin suna ɓoye takardun kuɗi a gida ba duk da karancin sabbin kuɗin. 

Shugaban EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa, ne ya bayyana haka yayin hira da Channels tv cikin shirinsu mai taken, The 2023 Verdict, ranar Laraba.

Ya kuma jaddada cewa doka ta baiwa kowane ɗan Najeriya dake tattare da tsoffin takardun naira ya maida su babban bankin Najeriya (CBN) a duk lokacin da ya so. 

Post a Comment

0 Comments