Advertisement

Responsive Advertisement

An Tafka Asarar Dukiyoyin Miliyoyin Naira Sakamakon Gobara A Kasuwar Yan Katako Na Anambra


Mummunan gobara ta yi barna a kasuwar yan katako na Umoukpa da ke jihar Anambra inda ta kone a kalla shaguna guda 17 Cif Martin Agbili, 

shugaban hukumar kashe gobara na jihar Anambra ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa ba a san sanadi ba 

Agbili ya ce jami'an hukumarsa sun yi nasarar kashe gobarar sun kuma hana ta bazuwa wasu shagunan amma an yi asarar dukiya 

Jihar Anambra - Gobara ta faru a kasuwar yan katako na Umoukpa, Awka, Jihar Anambra, inda ta lalata shaguna a kalla 17 a yankin a ranar Takata, rahoton The Punch. 

Duk da cewa ba a rasa rai ba, an tattaro cewa gobarar ta tashi ne misalin karfe 10.16 na dare kuma ta cigaba da ci har sai da jami'an hukumar kashe gobara na jihar suka taho wurin. 

Ba a iya sanin sanadin gobarar ba, amma shaidun gani da ido da wadanda abin ya shafi shagunansu sun ce gobarar ta lalata dukiyoyin miliyoyin naira.

 Shugaban hukumar kashe gobara na jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin Da ya ke tabbatar da lamarin

shugaban hukumar kashe gobara, Cif Martin Agbili, ya ce jami'ansa sun yi yaki da wutan har sai da suka ci galaba suka hana gobarar bazuwa. 

Misalin karfe 10.16 na daren ranar Talata, jami'an hukumar kashe gobara na jihar Anambra, sun samu kiran neman dauki sakamakon gobara a kasuwar katako na Umuokpu Awka. 

"Nan take muka tura motar kashe gobara da jaruman masu kashe gobara zuwa wurin. Daga bisani an kashe wutan cak. "Ba a san abin da ya janyo gobarar ba kuma ba a rasa rai ba. 

Kimanin shaguna 17 suka kone sosai amma an iya dakatar da gobarar daga bazuwa zuwa wasu shaguna. 

Post a Comment

0 Comments