Advertisement

Responsive Advertisement

Babban Gangamin Legas: Da Daske Tinubu Ya Watsa Wa Mutane Sabbin Kudi, APC Ta Fayyace Gaskiya


 Jam'iyyar APC ta karyata rahoton da ya bayyana dan takararta, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya watsa kudi ga taruwar jama'a a Lagos Seye Oladejo, 

mai magana da yawun APC reshen Jihar Lagos, ya ce yan adawa ne suka shirya hakan 

Oladejo ya kara da cewa an kirkiri rahoton don bata Tinubu a idon yan Najeriya wanda ke shan wahala saboda chanjin kudi 

Legas, Najeriya - Jam'iyyar APC reshen Jihar Lagos ta yi watsi da rahoton da ke cewa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar,

 Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya watsa wa mutane sabbin kudade a wurin taro a ranar Talata, 21 ga Fabrairu.

 Tinubu yana Lagos don rufe yakin neman zabe da ya gudana a filin wasa na Teslim Balogun, Surulere, Legas. 

A wata sanarwa da aka aikowa Legit.ng ta bakin mai magana da yawunta Seye Oladejo, jam'iyyar APC reshen Jihar 

Lagos ta ce batun Tinubu ya watsa kudi a taron ba komai ba ''face karya daga wajen mutanen banza''. 

A wani rahoto da ke yawo a halin yanzu, ya bayyana yadda Asiwaju Tinubu ya ke watsa damin kudade ga taruwar mutane a Oshodi yayin da tawagarsa ke wucewa daga filin jirgin saman 

Lagos zuwa filin wasa na Teslim Balogun, Surulere, Lagos,'' kamar yadda wani bangaren sanarwar ya shaida.

 Shiri ne don cutar da takarar Tinubu - APC Legas 

Jam'iyyar APC reshen Jihar Lagos ta kara da cewa rahoton ''bangare ne na irin mummunan shirin da ake yi don bata Tinubu a idon miliyoyin yan Najeriya da suka samun kudaden da ke ajiye a banki da suka sha wahalar tarawa.''

Post a Comment

0 Comments