Advertisement

Responsive Advertisement

Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC, Bola Tinubu Ya Dura Legas Don Halartar Wani Muhimmin Taro

Dan takarar shugaban kasa a APC, Asiwaju Bola Tinubu ya gana da shugabannin Yarbawa da na yankin Kudu maso 

Yamma gabanin zabe An ce Tinubu ya dura jihar Legas ne domin halartar wannan ganawa a ranar Litinin 20 ga watan Faburairun wannan shekarar 

'Yan siyasa da jam'iyyunsu na ci gaba da kira ga kowa da ya fito a yi zaben 2023 dashi don kawo shugaba ba gari 

Jihar Legas – Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya dura jihar Legas a ranar Litinin 20 Faburairu, 2023. 

A cewar Jubril Gawar, wani hadimin gwamna Babajide Sanwo-Olu, Tinubu ya dura ne a otal Eko don halartar wani taron 

Yarbawa da shugabannin yankin Kudu maso Yammacin kasar nan.

 Shugaban kasan Najeriya mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya iso otal dn Eko don ganaawa da shugabannin Yarbawa da na Kudu maso Yamma.”

Ku dage ku zabi Tinubu: Shawarin APC ga 'yan Najeriya baki daya a zaben bana 

A bangare guda, jam'iyyar APC ta bayyana bukatar 'yan Najeriya su maida hankali tare da ba Tinubu kuri'unsu a zaben 2023 da ke tafe nan kusa. 

Jam'iyyar ta bayyana cewa, Tinubu ne zai kawo karshen duk wani yanayi da kasar ke ciki tare da warware komai yadda ya kamata. 

Post a Comment

0 Comments