Advertisement

Responsive Advertisement

Kwankwaso Ya Tashi da Kuri’a 1 Kacal Yayin da Atiku Ya Kawowa PDP Akwatinsa


 ‘Dan takaran Shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya yi zarra a rumfarsa 

A akwatin yankin Jada inda Wazirin Adamawa yake zabe, ba a maganar kowa sai jam’iyyar PDP 

Bola Tinubu ya samu kuri’a 57, sai Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suka zo na uku da na Hudu 

Adamawa - Atiku Abubakar mai neman takarar shugabancin Najeriya a karkashin babbar jam’iyyar PDP ya samu galaba a akwatin zabensa. 

Jami’in zaben hukumar INEC na rumfar zaben da ke garin Jada, Nalawu Phillip ya tabbatar da cewa Atiku Abubakar ya samu kuri’u 282 a zaben. 

Daily Trust ta ce wanda ya zo na biyu shi ne ‘dan takaran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu. APC da Asiwaju Bola Tinubu sun samu kuri’u 57. 

Post a Comment

0 Comments