Advertisement

Responsive Advertisement

Mafarauci Ya Bankado Dubban Katunan Zabe a Dajin Anambra


 Yan kwanaki kafin babban zaben shugaban kasa, wani mafarauci a jihar Anambra ya zakulo katunan zabe masu yawan gaske a wani jeji 

Rahoto ya nuna cewa mafaraucin ya bankado dubban katunan zabe da aka zuba a wata jaka sannan aka jefa ciki duron a yankin Nnewi 

Rundunar yan sanda ta yi martani kan lamarin inda ta ce ta shiga bincike don gano gaskiyar lamari

Rahotanni sun kawo cewa wani mafaruci ya tsinci dubban katunan zabe na PVC a wani jeji da ke yankin Nnewi na jihar Anambra. 

Amaka Nwafor, wata mai gabatar da shirye-shirye a Authority FM, ta ce wani mafarauci ya tsinci katunan zabe a ranar Talata, a jejin Akamili, karamar hukumar Nnewi ta arewa, rahoton The Cable.

Ta ce katunan zaben sun kasance a cikin wasu jakunkuna biyu sannan an jefa su a cikin wata bakar randa, tana mai cewa bayan ya gano su, sai mafaraucin ya kai su harabar gidan radiyon.

Nwafor ta ce katunan zaben da aka duba zuwa yanzu mallakin al'ummar yankin karamar hukumar Nnewi ta arewa ne. 

Post a Comment

0 Comments