Mutum 5500 suka kada kuri’arsu a wannan zabe da aka shirya wanda aka yi kusan kwana biyu ana fafatawa.
A karshe Jam’iyyun APC da PDP da ‘yan takaransu Bola Tinubu da kuma Atiku Abubakar ba su je ko ina ba
Asiwaju Bola Tinubu ya zo na karshe a ra’ayin jama’a, ya samu kuri’u 588 ne da ke wakiltar kashi kusan 10%.
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ‘dan takaran PDP a 2023, ya samu kuri’un mutane 856 a cikin 5590.
Rabiu Kwankwaso wanda ya tsaya a jam’iyyar adawa ta NNPP, shi ya yi zarra da farko, ya kare da kusan 28%
Idan za a bi ra’ayin masu binmu a dandalin Twitter, Peter Obi ne zai lashe zaben shugaban kasar Najeriya
0 Comments