Advertisement

Responsive Advertisement

Na Ga Peter Obi Yana Kuka: Cewar Fasto Daniels Yayin da Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben 2023


 Bishop Feyi Daniels na cocin IReign Christian Family ya yi hasashen cewa Bola Tinubu na APC ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2023

 Malamin addinin ya bayyana cewa an nuna masa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP yana kuka saboda ya fadi zabe

 A cewar Faston, Atiku Abubakar ba zai taba shugabancin Najeriya ba kuma ya fada masa haka a 2019 

Bishop Feyi Daniels, babban fasto a cocin IReign Christian Family, ya yi wasu hasashe cewa za a sanar da dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe mai zuwa.

 A wani bidiyo da ya yadu, malamin addinin ya ce an nuna masa Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Ya kuma ce a wahayin da aka masa, ya ga abun da Tinubu ya sanya yana mai nuni ga yadda yake ta yi.

 Na Ga Peter Obi Yana Kuka: Cewar Fasto Daniels Yayin da Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben 2023 Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Atiku bubakar, Peter Obi Asali:

 Twitter Tinubu na daya daga cikin manyan yan takara a zaben shugaban kasar. Sauran manyan yan takara sun hada da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party.

Post a Comment

0 Comments