Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce babu nagarta a babban zaษen ฦasar da aka yi ranar Asabar a don haka ya ce dole ne a soke shi a yankunan da aka yi tashin hankali.
Ya buฦaci Shugaban Hukumar zaษe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da ya ceci Najeriya daga faษawa haษarin rikici.
Tsohon shugaban ฦasar ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya yi wa taken "Zaษen Shugaban Najeriya na 2023: Rokon A yi taka tsan-tsan da kuma gyara.''
Obasanjo ya ce ba wani abin sirri ne, cewa an zargi wasu daga cikin ma'aikatan hukumar zaษen da suka gudanar da aikin sun bayar da kai sakamakon aika alkaluman zaษen ba ta hanyar na'ura ba, abin da ya sa ake zargin wani sakamkon an ฦirฦire shi ne.

Comments
Post a Comment