Wakilin jam'iyyar PDP a dakin tattara sakamakon zaben shugaban ฦasa, Sanata Dino Melaye ya yi ฦorafin cewa an tafka maguษi a sakamakon zaษen shuagaban ฦasa na jihar Ekiti.
Dino Melaye ya yi ฦorafin a gaban shugaban hukumar zaษe farfesa Mahmood Yakubu, inda ya ce INEC ta sake duba batun kuri'un jihar.
Melaye ya kuma yi korafin cewa INEC ba ta saka sakamakon zaษe a cikin rumbun bayananta na intanet.
Sai dai, farfesa Yakubu ya mayar da martanin cewa alkaluma da wakilin na PDP ya bayyana hukumar bata san da su ba saboda waษanda ke hannunta sahihahi ne.
Jam'iyyar PDP ta ce hukumar INEC ta saba wa doka wajen rashin sanya sakamakon zaben shugaban kasa a manhajarta ta intanet.

Comments
Post a Comment