Wani tsohon minista ya nuna kwarin gwiwa cewa dan takarar PDP, Atiku Abubakar, zai lashe babban kaso a arewa maso gabas
Tsohon karamin ministan shari'a kuma mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Musa Elayo, ya nuna yakinin cewa dan takararsu zai lashe zabe a arewa ta tsakiya, rahoton Leadership.
Gabannin babban zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu, masu nazari kan harkokin zabe sun bayyana arewa ta tsakiya a matsayin filin daga ga manyan yan takarar babban kujera ta daya a kasar.
Tsohon minista ya bayyana yankin da Atiku zai lashe
A yanzu haka, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ce ke iko a jihohin yankin baya ga Benue, inda Samuel Ortom na PDP ke a matsayin gwamna.
A wata hira da ya yi da jaridar Leadership a garin Lafiya, jihar Nasarawa, a ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu, Elayo ya ce: "Saboda haka, ina hango haske ga PDP a jihohin arewa ta tsakiya a wannan zaben mai zuwa."
Ina nan a PDP ba zan koma APC ba, Gwamna Wike A wani labari na daban, gwamnan jihar Ribas, Nyesom
Wike ya bayyana cewa yana nan daram dam a PDP cewa karya ne baya shirin komawa APC kamar yadda ake ta hasashe
Ba Zata Saɓu Ba, Korarren Sanatan PDP Ya Bayyana Matsayin Takarar Sa a Zaɓe... Da yake magana a ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu,
Wike ya ce shakka babu halin dattako na jam'iyyar APC ya matukar burge shi domin sun tsaya tsayin daka a kan mulkin karba-karba.
A cewarsa gwamnonin jam'iyyar mai mulki sun jajirce sai da aka mika tikitin shugaban kasa ga yankin kudu kamar yadda suka yi yarjejeniya tun daga farko.
0 Comments