Advertisement

Responsive Advertisement

Wani Kamfanin Kasar Sin Ya Ba Ma’aikata Kyautar Tulin Tsabar Kudi, Bidiyo Ya Girgiza Intanet


 An ga wani bidiyon ma’aikata na karbar kyautar kudi daga kamfaninsu ya yadu a kafar sada zumunta, ya jawo cece-kuce

 An ce mutum uku da suka fi kokari a kamfanin sun samu kyautar Yuan miliyan biyar kowannensu, kwatankwacin N334.7m 

Wannan babbar kyauta ta girgiza jama’ar kafar sada zumunta, sun kuma yi mamakin karamcin wannan kamfanin 

Wani bidiyo ya yi shuhura a kafar sada zumunta na wasu ma’aikatan kamfanin Henan a kasar Sin, inda aka ba su kyautar karshen shekara na tsabar kudade a hannu. 

An ba mutanen ne tulin takardun kudade tsaba a hannu, inda ma’aikatan da kansu suka shiga mamaki da ta’ajibi. 

A cewar rahoton jaridar South China, mutum biyar da suka fi kokari a kamfanin sun samu kyautar 

Yuan miliyan biyar, kwantankwacin N334.77m kowanne daga cikin kyautar kudi Yuan mikiyan 61 (N4.08bn) da kamfanin ya yi. 



Post a Comment

0 Comments