Kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta bayyana rashin amince da kashe tsoffin kudi duk da umarnin kotu da na CBN
Wannan na zuwa ne a ranar Litinin, inda aka tattauna da wani shugaban kungiyar kan matsayarta a wannan karon
Tun bayan kawo batun sauyin Naira, an sha samun cece-kuce da sabani tsakanin ‘yan Najeriya da bankunan kasar nan
Najeriya - Dillalan man fetur a ranar Litinin sun ci gaba da bayyana rashin amincewarsu da karbar tsoffin takardun Naira daga hannun mutane, duk da cewa CBN ya ba da umarnin a ci gaba da karbar kudin.
An kuma tattaro cewa, har yanzu bankuna basu yi magana da dillalan mai da masu gidajen mai ba game da ci gaba da karbar tsoffin kudin a Najeriya, Punch ta ruwaito.
0 Comments