Hukumar Zaษe ta Najeriya INEC ta ษage zaษen gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi da mako guda, wato zuwa 18 ga watan Maris
INEC ta tabbatar wa da BBC ษage zaษen, bayan wani taron sirri da manyan jami'an hukumar suka yi a Abuja.
Kafofin yaษa labarai na Najeriya sun ambato cewa INEC ba ta kammala saita na’urar tantance masu zaษe ba ta BVAS wadda aka yi amfani da ita a zaษen shugaban ฦasa a ranar 25 ga watan Fabirairu.
Sun ฦara da cewa hukumar ta ce sai ta samu damar kwashe bayananta da ta tattara na a yayin zaษen shugaban ฦasar zuwa wani rumbunta na daban kafin ta sake saita na’urar ta yadda za a yi zaษen gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi ba tare da wata damuwa ba.

Masha Allah
ReplyDelete