Azumin Ramadan lokaci ne da al'ummar Musulmi a faษin duniya ke zage damtse don yin ayyukan da za su inganta imaninsu tare da kyautata wa ฦดan uwa da abokan arziki duk domin neman tsira da samun lada.
ฦaya daga cikin abubuwan kyautatawa da ke ฦara yawan lada a wannan lokaci shi ne ciyarwa kuma bisa al'ada, mata a gidaje sukan yi tanadi don girka abinci iri-iri da nufin faranta ran mai gida da ฦดaฦดa har ma da abokan arziki.
Sai dai a lokacin dafa abincin buษa-baki, wasu mata kan yi shakku wajen tabbatar da ko ษanษanon girkinsu ya yi daidai, kasancewar yanayin azumi da suke ciki.
BBC ta tuntuษi Malaman addinin Musulunci don jin hukuncin ษanษana abinci a yayin azumi.
Malama Fatima Laminu, wata malamar addinin Musulunci a Abuja, ta ce babu laifi idan aka ษanษana abinci matuฦar "mutum ba zai bari yawun ya wuce zuwa maฦogwaronsa ba."
Ta ce sai dai yin hakan na iya zama kuskure idan aka yi da ganganci har abincin ya wuce maฦogwaro, wanda idan hakan ta faru, toh ya zama dole mutum ya rama azumi.
Ta ce hanya mafi sauฦi ga mai azumin da ke son ษanษana girki, ita ce ya furzar da duk abin da ya ษanษana kafin ya tafi cikin maฦoshi.
Sai dai ta ce an samu saษani tsakanin malamai game da mai azumin da ya ษanษana abinci har ya wuce maฦogwaro, amma ba da saninsa ba.
A cewar Malama Fatima, "wasu malaman sun ce, mutum zai kai azumin sannan kuma ya rama, wasu kuma sun ce tun da kuskure ne, in dai a kan mantuwa ne, ba abin da ya samu azuminsa, wato dai azuminsa yana nan."

Comments
Post a Comment