Advertisement

Responsive Advertisement

Ministan Buhari Ya Fayyace Komai Bayan An Ga Babu Sunansa Cikin Lauyoyin Tinubu


 Da farko an yi tunanin Festus Keyamo SAN yana cikin Lauyoyin da za su ba Bola Tinubu kariya 

Lauyan ya ce tun da shi Minista ne, ba zai iya tsayawa ‘dan takaran ba sai ya sauka daga kujera 

Ganin cewa ba a ga Festus Keyamo SAN a jeringiyar Lauyoyin da za su tsayawa Asiwaju Bola Tinubu a kotun zabe ba, wannan ya jawo abin magana. 

Lauyan ya yi amfani da shafinsa na Twitter a ranar Talata, ya fadi abin da ya ba zai iya kare ‘dan takaran APC kuma zababben shugaban kasar a kotu ba. 

Keyamo ya nuna a matsayinsa na wanda yake rike da mukami a gwamnatin tarayya, bai da damar da zai shiga kotu domin ya ba daidaikun mutane kariya. 

RECOMMENDED FOR YOU 

Da Ɗumi-Dumi: Jiragen Rundunar Sojin Sama Guda Biyu Sun Yi Hatsari, An Rasa... 

Babu ruwan Minista da karar zabe Tun a 2019 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Lauyan a matsayin Minista a ma’aikatar Neja-Delta, daga baya ya koma ma’aikatar kwadago.

Post a Comment

0 Comments