Advertisement

Responsive Advertisement

Uefa za ta biya 'yan Liverpool kudin tikitin Champions League


 Uefa za ta biya kudin tikitin magoya bayan Liverpool, wadanda suka saya don kallon wasan karshe a Champions League a Paris a 2022.

Hakan ya biyo bayan wani kwamiti mai zaman kansa da ya binciko cewar Uefa ce ta haddasa turmutsitsin da ya faru, kafin wasan karshe tsakanin Liverpool da Real Madrid.

Magoya baya da dama ba su samu damar shiga kallon wasan ba, an kuma bada barkonon tsohuwa a fafatawar da aka yi lattin minti 36 kan fara wasan.

Uefa ta ce za ta biya dukkan tikiti 19, 618 da aka bai wa magoya bayan liverpool, domin kallon fafatawar da aka yi a Faransa.

Post a Comment

0 Comments