Advertisement

Responsive Advertisement

A ranar Juma'a ko Asabar Musulmin duniya za su yi bikin Ƙaramar Sallah. Ƙarin bayani 👇👇👇



Wata cibiya mai nazarin kimiyyar taurari da ke birnin Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, ta ce ba lallai ne a ga watan Shawwal ba a ranar Alhamis, inda ta ce hakan na nufin cewa sai ranar Asabar za a yi sallah Eid Al-Fitr. 

A wata sanarwa da cibiyar ta International Astronomical Center ta fitar a shafinta na Twitter, ta ce ta yi hasashen ne bayan tattara bayanai, inda ta ce hukumomin da aka ɗora wa alhakin duba wata, su ne kaɗai za su bayyana ganinsa da kuma ranar da za a yi sallah.

"Ganin jinjirin watan ranar Alhamis da yamma yana da matukar wahala domin yana bukatar na'urar hangen nesa, in ji wani kwararre mai lura da yanayi na musamman.

Cibiyar ta ce ganin jinjirin watan ba zai yiwu ba ranar Alhamis a ko’ina a galibin ƙasashen Larabawa, in ban da wasu sassan yammacin Afirka. 

Cibiyar ta ce ba a sa ran ganin watan ko da ta hanyar amfani da na'urar hangen nesa ne. Don haka a ranar Juma'a ne akasarin ƙasashen Musulmi za su sanar da ganin watan Shawwal.

 

Post a Comment

0 Comments