Advertisement

Responsive Advertisement

Zan yi nesa da Abuja idan na sauka daga mulki - Buhari


 Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai koma garin mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina, idan ya miƙa ragamar mulki ga sabuwar gwamnati mai zuwa a ranar 29 ga watan Mayu. 

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar, ya ce Buhari ya faɗi haka ne jiya Laraba lokacin da ya karɓi bakuncin Jakadiyar Birtaniya a Najeriya mai barin gado, Catriona Wendy Laing. 

Buhari ya yaba wa ƙasar Birataniya kan tallafa wa Najeriya a ɓangarori da dama da take musamman ma wajen sake gina yankin arewa maso gabas da ayyukan ƴan ta da ƙayar-baya ya ɗaiɗaita. 

Ya ce Birtaniya ta kasance gida ga ƴan Najeriya da dama, inda ya ce dangataƙar ƙasashen biyu za ta ci gaba da wanzuwa. 

Tun da farko, Jakadiyar Birtaniyan ta ce ba ta jin daɗi ganin cewa za ta bar Najeriya, musamman ma ganin cewa ta ga abubuwa da dama a ƙasar kama daga al'adu da raye-raye da kuma wakokin ƴan ƙasar masu daɗi.

Ta ce ta ji daɗin kasancewarta a Najeriya, inda ta ce ta ziyarci jihohi sama da 20. Ta ce "na faɗa wa wanda zai gaje ni da shi ma idan ya zo ya rika yin irin abubuwan da nayi.

Ta kuma yaba wa shugaba Buhari kan samun nasarar kammala wa'adin mulkinsa na shekara takwas, inda ta ce ya yi kokari matuka wajen tafiya da ƴan ƙasar gaba-ɗaya.

Post a Comment

0 Comments