A karshen makon nan dai wahalar man fetur ta kara bazuwa a Legas, babbar hedikwatar kasuwancin kasar, inda yanzu haka take ci gaba da tsananta ganin yadda cewa masu ababen hawa na kwana a gidajen mai.
Rahotannin da wakilinmu ya samu a birnin Ikeja da kewaye ya nuna cewa a yanzu haka an rufe akasarin gidajen mai, inda aka ce sun kare ne yayin da wasu kadan ke rarrabawa.
A dukkan gidajen mai da wakilinmu ya ziyarta, ya lura da dogayen layukan da suka kai kusan mita 500 zuwa kilomita daya a yayin da masu ababen hawa ke fafutikar neman mai.
Wadanda abin ya shafa sun hada da ‘yan kasuwa da masu motocin masu zaman kansu wadanda suka koka da shafe sa’o’i masu yawa a kan layukan shan mai.
A wani gidan mai na Mobil da ke kan titin Obafemi Awolowo daura da fitaccen shatale-talen Allen da ke birnin Ikeja, akwai jerin gwanon motoci da ke layin shan mai da ya zarce shatale-talen har zuwa titin Aromire.
0 Comments