Karancin Naira: Kwastomomi Sun Banka wa ATM Wuta a Jihar Legas
Daga karewar kudi, wasu fusatattun kwastomomi sun cinna wa na'urar cire kuษi a banki ATM wuta a jihar Legas Jami'in hulษa da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya ce tuni dakarun yan sanda suka shawo kan lamarin Tun bayan sauya fasalin naira, yan Najeriya sun tsinci kansu cikin wahala saboda rashin wadatar sabbin kuษi Lagos - Wasu fusatattun kwastomomi sun bankawa na'urar ATM wuta a wani banki da ba'a bayyana ba a yankin Idi Araba, jihar Legas bayan kuษin da ke ciki sun ฦare. Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin dai ya kawo tsaiko a harkokin bankin domin sai da ta kai ga aka tura jami'an yan sanda kai ษauki. Karancin Naira: Kwastomomi Sun Banka wa ATM Wuta a Jihar Legas Hoto: dailytrust Asali: UGC Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce zaman lafiya ya dawo a yankin. Sai dai mai magana da yawun yan sandan bai bayyana sunan bankin da...



