Daga karewar kudi, wasu fusatattun kwastomomi sun cinna wa na'urar cire kuษi a banki ATM wuta a jihar Legas
Jami'in hulษa da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya ce tuni dakarun yan sanda suka shawo kan lamarin
Tun bayan sauya fasalin naira, yan Najeriya sun tsinci kansu cikin wahala saboda rashin wadatar sabbin kuษi
Lagos - Wasu fusatattun kwastomomi sun bankawa na'urar ATM wuta a wani banki da ba'a bayyana ba a yankin Idi Araba, jihar Legas bayan kuษin da ke ciki sun ฦare.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin dai ya kawo tsaiko a harkokin bankin domin sai da ta kai ga aka tura jami'an yan sanda kai ษauki.
Karancin Naira: Kwastomomi Sun Banka wa ATM Wuta a Jihar Legas Hoto: dailytrust Asali: UGC Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Legas,
SP Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce zaman lafiya ya dawo a yankin.
Sai dai mai magana da yawun yan sandan bai bayyana sunan bankin da lamarin ya shafa ba, haka zalika bai ce komai ba game da kama waษanda suka aikata ษanyen aikin ba.
Da safiyar nan a yankin Idiaraba, kuษi suka kare a ATM mutane suka fusata suka banka masa wuta.
Nan take jami'ai daga Caji Ofis mafi kusa suka kai ษauki wurin." "Tuni aka kashe wutar kuma an shawo kan mutanen da ke wurin kuma tun lokacin harkokin bankin ya ci gaba kamar yanda aka saba." - Benjamin Hundeyin.
Tribune Online ta tattaro cewa zanga-zanga ta ษarke da sassan Najeriya a 'yan kwanakin nan sakamakon wahalhalu da karancin naira.
Da yawan 'yan Najeriya sun wayi gari cikin yanayin damuwa bayan babban bankin Najeriya ya sauya fasalin N200, N500 da N1000 kuma sabbin basu wadata ba.
Fusatattun kwastomomi sun ฦone Bankuna da yawa a bangarori daban-daban na ฦasar nan saboda rashin samun damar cire kuษi daga asusun bankunansu.

Comments
Post a Comment