Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai koma garin mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina, idan ya miฦa ragamar mulki ga sabuwar gwamnati mai zuwa a ranar 29 ga watan Mayu.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar, ya ce Buhari ya faษi haka ne jiya Laraba lokacin da ya karษi bakuncin Jakadiyar Birtaniya a Najeriya mai barin gado, Catriona Wendy Laing.
Buhari ya yaba wa ฦasar Birataniya kan tallafa wa Najeriya a ษangarori da dama da take musamman ma wajen sake gina yankin arewa maso gabas da ayyukan ฦดan ta da ฦayar-baya ya ษaiษaita.
Ya ce Birtaniya ta kasance gida ga ฦดan Najeriya da dama, inda ya ce dangataฦar ฦasashen biyu za ta ci gaba da wanzuwa.
Tun da farko, Jakadiyar Birtaniyan ta ce ba ta jin daษi ganin cewa za ta bar Najeriya, musamman ma ganin cewa ta ga abubuwa da dama a ฦasar kama daga al'adu da raye-raye da kuma wakokin ฦดan ฦasar masu daษi.
Ta ce ta ji daษin kasancewarta a Najeriya, inda ta ce ta ziyarci jihohi sama da 20. Ta ce "na faษa wa wanda zai gaje ni da shi ma idan ya zo ya rika yin irin abubuwan da nayi.
Ta kuma yaba wa shugaba Buhari kan samun nasarar kammala wa'adin mulkinsa na shekara takwas, inda ta ce ya yi kokari matuka wajen tafiya da ฦดan ฦasar gaba-ษaya.
