Gwamnatin Habasha ta saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da dakarun Tigray da ke arewacin ƙasar a watan Nuwamban bara, a wani mataki na kawo ƙarshen yaƙin basasar da aka shafe shekaru biyu ana fafatawa.
Sai dai, kungiyoyin ba da agaji da mazauna yankin, sun faɗa a Labarai cewa ana ci gaba da far wa fararen hula - musamman ma cin zarafin mata.
Wannan labari na ɗauke da abubuwan da za su tayar da hankalin masu karatu wanda ya haɗa da cin zarafin mata.
A ranar da gwamnatin Habasha ta sha hannu da abokan adawarsu daga yankin Tigray don cimma yarjejeniyar zaman lafiya – dukkan bangarori na cikin annashuwa – Letay kuwa ta shafe tsawon daren ɓoye a karkashin gada, inda take jin yadda ƙarar harbin makamai a kusa da ita.
"Bayan faruwar lamarin, na yi wata dogon tsuma kafin na dawo cikin hayyacina. Na ɓoye kaina har sai da sojojin suka tafi.’’
Mun sauya sunan Letay da wasu waɗanda aka yi wa fyaɗe da suka faɗa wa labarai , don kare su daga tsangwama da ɗaukar fansa.
A cikin shekara biyu da aka ɗauka ana yaƙi a arewacin Habasha, kungiyoyi da dama da suka haɗa da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin ƙare hakkin ɗan adam da kuma ‘yan jarida, sun ɗauki bayanai na yadda sojojin Eriteria da ƙawayensu da kuma mayaƙa suke yi wa mata fyaɗe.
An kuma zargi dakaru daga Tigray da yi wa mata fyaɗe a yankin Amhara a kokari da suke yi na dannawa zuwa babban birnin ƙasar.
0 Comments