Zaษaษษun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a sassan duniya a makon da ya gabata
Wasu mata a birnin Legas na Najeriya kenan a lokacin da suke gudanar da bikin ranar mata ta duniya ranar Laraba
Mata da dama ne suka fito domin nuna murna murna a bikin ranar matan da Majalisar Dinkin Duniya ta ware kowacce ranar 8 ga watan Maris
Wannan matar na yi wa ษanta wasa a unguwar Mathare da ke birnin Nairobi na ฦasar Kenya.
Daliban jami'ar Witwatersrand da ke Afirka ta Kudu sun yi zanga-zangar neman neman taimako ga ษaliban da ba su da ฦarfin biyan kuษin makaranta.
Hukumomin jami'ar sun mayar da martani ga buฦatar ษaliban, inda suka ce za su faษaษa tallafin da suke bai wa ษaliban marasa ฦarfi a jami'ar
Waษanan matan sun halarci bikin nuna fulawoyi da ake gudanarwa shekara-shekara a birnin Khartoum da aka gudanar ranar Asabar
Ranar Asabar shugaban Faransa Emmanuel Macron ya samu gagarumar tarba a binin Kinshasa, na jamhuriyar Dimokraษiyyar Kongo, a lokacin wata ziyara da ya kai domin sake inganta dangantaka tsakanin Faransa da nahiyar Afirka.
Mai sayar da fitilu a kasuwa Giza da ke ฦasar Masar ranar Talata. Ana sayar da fitilun ne gabanin watan Ramadan da musulmi a faษin duniya za su gudanar da azumin watan.
Gabanin ฦara wa'adin riga-kafin cutar zazzaษin cizon sauro da ake yi wa yara , makaษa na amfani da abubuwan bushe-bushe na zamani a garin Gisambi na ฦasar Kenya. Ana gudanar da riga-kafin a ฦasashen Ghana da Kenya da Malawi, kuma kawo yanzu an yi wa yara fiye da miliyan ษaya tun shekarar 2019 kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana.









Comments
Post a Comment