Advertisement

Responsive Advertisement

Jam’iyyar APC na takaicin rashin kujerar gwamnan Kano


 Jam`iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta ce tana jin takaicin kayen da jam`iyyar NNPP ta yi mata a jihar Kano a zaben gwamnan da ya wuce. 

Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya shaida wa BBC cewa, babban abin bakin ciki shi ne a ce sun rasa Kano.

Ya ce, “ Kamar Kano, a ce mun rasa Kano, to amma laifin wasu ne ya sa muka fadi a Kanon.”

Shugaban na APC, ya ce “ Akwai wadanda ba su yi abin da ya kamata ba, ga shi a yanzu ya sanya ‘ya’yan jam’iyar cikin wani hali saboda nasarar da jam’iyyar ba ta samu ba, bayan ga shi su sun yi duk abin da ya kamata su yi.”

Post a Comment

0 Comments