Advertisement

Responsive Advertisement

Wata mata ta gurfanar da mijinta a kotu saboda ya ki kai ta Saudiyya


Wata mata mai shekaru 45, mai suna Karima Nuhu, a ranar Talata ta maka mijinta, Musa Falalu, a gaban wata kotun shari’ar musulunci da ke Rigasa, a jihar Kaduna, bisa zargin kin kai ta ƙasar Saudiyya. 

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa matar wadda ke zaune a unguwar Rigasa, ta shaida wa kotun cewa ta yi aure da Falalu tsawon shekara huɗu, amma abinci na tsawon wata biyu kaɗai ya ba ta tun bayan yin auren. 

“Ya faɗa min cewa ya rasa aikinsa na direba amma ya samu wani a Saudiyya, inda ya bukace ni da in yi hakuri da kuma yin alkawarin tafiya da ni," in ji matar. 

“A yanzu, ni ke ciyar da kaina. Har ma na ara masa kuɗi domin ya samu biyan kudin tafiyar, amma bayan samun abin da yake so sai ya sake ni,” inji ta. 

Ta shaida wa kotun cewa Allah zai mata sakayya tsakaninta da mijin a gobe kiyama. 

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta zargin, inda ya shaida wa kotu cewa ya saki matar tasa. 

Alkalin kotun, Malam Anass Khalifa, wanda ya tabbatar da rabuwar aure tsakanin ma’auratan, ya ce kotun za ta saurari korafe-korafen matar ne idan da a ce ta gansu.


 

Post a Comment

0 Comments