Advertisement

Responsive Advertisement

Kai Tsaye: Yadda Gangamin Kamfen Din Tinubu/Shettima Ke Gudana A Lagas


Yadda Gangamin Kamfen Din Tinubu/Shettima Ke Gudana A Lagas Talata, Faburairu 21, 2023 at 3:16
 Yamma daga  Aisha Musa A yau Talata, 21 ga watan Fabrairu ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), zai gudanar da gangamin kamfen dinsa na karshe a filin wasa na Teslim Balogun Stadium (TBS) da ke jihar Lagas.
 Tun bayan da ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na APC, Tinubu ya gudanar da gangamin kamfen guda biyu a jihar da ya mulka a matsayin gwamna.
 Kai Tsaye: Yadda Gangamin Kamfen Din Tinubu/Shettima Ke Gudana A Lagas Asali: Original Ana sanya ran Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai jagoranci dukkanin gwamnonin jam'iyyar mai mulki da sauran masu ruwa da tsaki zuwa TBS gabannin babban zaben na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu. 
Wasu masu lura da harkokin siyasa suna ganin cewa wannan gangamin na da matukar muhimmanci ga Tinubu saboda dole ya dakushe manyan abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party wadanda suka gudanar da manyan gangami a Lagas.

Mazauna Legas sun kai Tinubu wajen gangamin kamfen din APC Dubban mazauna jihar Lagas sun yi wa tsohon gwamnansu kuma dan takarar shugaban kasa APC, Bola Tinubu, rakiya har zuwa wajen gangamin kamfen din jam’iyyar da ke gudana a TBS. 
Tare da shi akwai mataimakinsa, Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da kuma kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Buhari ya isa jihar Legas don yi wa Tinubu kamfen Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa filin wasa na kasa da ke Surulere don halartan gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na APC. 

Mai ba shugaban kasa shawara kan shafukan sadarwar zamani, Bashir Ahmad, ya saki bidiyo da ke nuna lokacin da jirgin shugaban kasar ya sauka a jihar Lagas. 

Post a Comment

0 Comments