Yayin da ya rage kasa da mako da guda a soma manyan zabuka a Najeriya, rundunar 'yan sandan yankin birnin tarayya Abuja ta ce ta shirya tsaf domin samar da tsaro a lokacin zabukan.
Mai Magana da yawun rundunar DSP Josephine Adeh, ta shaida wa Labarai cewa sun hada kai da Hukumar Zabe ta kasa da kuma sauran jami'an tsaro kamar sojoji don ganin anyi zabe lafiya ba tare da wata matsala ba.
Ta ce, "Mun ba wa jami’anmu horo da ma sauran jami’an tsaro a kan yadda za a samar da tsaro a yayin zaben.”
Jami’ar ‘yar sandar ta ce, tun kafin zaben ma sun tura jami‘ansu zuwa ofisoshin zabe don kare su, da kuma gano wuraren da suke gani za a iya samun matsala a lokacin zabe.
DSP Josephine Adeh, ta ce, "A Abuja babban birnin tarayyar Najeriya za mu zuba ‘yan sanda da dama, kamar yadda babban sifeton ‘yan sanda na kasa ya fada za a zuba jami’an tsaro fiye da dubu 400 a kasa baki daya.”
Ta ce, yayin da zaben ya taho sun rabawa kowane dan sanda da zai yi aiki a Abuja aikin da zai yi dama inda zai je.
Jami’ar ‘yar sandan, ta ce sun riga sun san ‘yan sanda nawa za su sanya a kowacce mazaba, akwai kuma masu jiran ko ta kwana.
"Baya ga dukkan wadan nan shirye-shiryen, mu da sauran jami’an tsaro muna nazari a kan irin abubuwan da suka faru a zabukan da suka wuce don mu gyara kasancewar shi zaben 2023 ya sha bambam da na baya saboda tabarbarewar tsaro.” In ji ta.
DSP Josephine Adeh, ta ce wani albishir kuma da za ta yi wa jami’ansu shi ne wadanda ba sa aiki a cikinsu za su iya zuwa su jefa kuri’arsu sabanin a baya da ba sa yi.
0 Comments