Advertisement

Responsive Advertisement

Taliban za ta mayar da sansanonin sojin waje cibiyoyin kasuwanci


Gwamnatin Afghanistan ta 'yan Taliban ta ce za ta sauya wasu daga cikin sansanonin sojojin ƙasashen waje da ke ƙasar zuwa cibiyoyin kasuwanci.

Afghanistan ta samu kanta cikin gagarumar matsala ta tattalin arziki da dagulewar rayuwar ja'ama tun bayan da Taliban ta sake karɓe iko da gwamnatin ƙasar a watan Agusta na 2021.

Sojojin ƙasashen waje sun kasance a ƙasar tsawon shekaru ashirin.

Muƙaddashin firaminista kan harkokin tattalin arziƙi Mullah Abdul Ghani Baradar shi ne ya bayar da sanarwar.


A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Mullah Baradar ya ce, ''An yanke shawarar cewa ma'aikatar harkokin kasuwanci da masana'antu za ta karɓi iko da ragowar sansanonin sojojin ƙasashen waje da nufin mayar da su cibiyoyin kasuwanci na musamman.''

Ya ƙara da cewa aikin zai fara ne da sansanonin da ke babban birnin ƙasar Kabul da kuma lardin Balkh na arewaci, amma kuma bai bayar da ƙarin bayani ba.

Muhammad Faizal Bin Abdul Rahman na makarantar nazarin harkokin ƙasashen waje ta S Rajaratnam a Singapore ya gaya wa BBC cewa, "Taliban na matuƙar buƙatar bunƙasa asusunta idan har za ta inganta yanayin shugabancinta kuma tana son samun karɓuwa ga jama'a sosai a cikin gida." 

Ya ƙara da cewa, "Mafi muhimmanci ma Taliban na buƙatar tabbatar da ƙudurinta a tsare-tsaren tattalin arziƙi.''

''Wannan kuwa ya haɗa da samar da yankuna masu zaman lafiya a kusa da babban birni da kuma kan iyakoki domin 'yan kasuwa masu zuba jari na waje kamar 'yan China... da kuma buƙatar farfaɗo da harkokin kasuwanci na yankin da maƙwabta," in ji masanin


An yi ƙiyasin cewa Afghanistan tana da albarkatun ƙasa waɗanda darajarsu ta kai dala tiriliyan ɗaya, waɗanda suka ƙunshi iskar gas da jan ƙarfe da makamantansu.

Sai dai yawancin waɗannan albarkatu ba a kai ga cin moriyarsu ba saboda tashin hankali na tsawon shekaru da ƙasar ke fama da shi.

A watan Agusta na 2021, jirgin sama na ƙarshe na sojin Amurka ya bar filin jirgin sama na Kabul, abin da kawo zaman Amurka na shekara 20 kuma yaƙinta mafi daɗewa ƙarshe.

Rikicin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallinsu.

Tun bayan ficewar sojin waje daga ƙasar harkar kuɗin Afghanistan ta gamu da manyan matsaloli.

An sanya takunkumi a kan jami'an gwamnatin kuma an dakatar da kadarorin babban bankin ƙasar da ke waje, sannan an dakatar da atallafin da ake bai wa ƙasar daga waje, wanda kusan shi ne tattalin arziƙin ya dogara da shi a baya.

A farkon wannan shekara gwamnatin ta Taliban ta ce ta shirya ƙulla yarjejeniya da wani kamfanin China domin haƙo mai a arewacin ƙasar.

Yarjejeniyar ta shekara 25 na nuna muhimmancin shigar China harkokin tattalin arziƙi a yankin.

Har yanzu gwamnatin China ba ta amince da gwamnatin Taliban ta Afghanistan ba, amma kuma tana da sha'awa sosai a kan harkokin ƙasar, wadda ke tsakiyar yankin da ke da muhimmanci ga faɗaɗa tasirin hina da kuma aikinta na samar da hanyoyi a yankin.

Aikin da Shugaba Xi Jinping ya ƙaddamar a 2013, ya samar da kuɗaɗe ga ƙasashe masu tasowa domin su gina abubuwan jin ɗadin jama'a kamar tasoshin jirgin ruwa da na sama da tituna da kuma gadoji.


 

Post a Comment

0 Comments