'Ina jin raษaษi idan na ga maza kawai suna zuwa makaranta ban da mu'
"Kowacce rana ina tashi ne da burin ganin na koma makaranta. Taliban sun yi ta faษin cewa za su buษe makarantu. Amma yanzu ga shi har shekara biyu babu wani labari.
Ban yarda da su ba. Ina jin takacin hakan,'' in ji Habiba ฦดar shekara 17
Ta kasance tana cizon yatsunta saboda da takaici.
Habiba tare da ฦawayenta Mahtab da Tamana na cikn dubban yara mata da Taliban ta haramta musu zuwa makaranta - ฦasa ษaya tilo da ta ษauki irin wannan mataki.
Shekara ษaya da rabi bayan faruwar lamarin, an katse musu rayuwa, inda har yanzu suke ci gaba da nuna takaici.
Fara zangon karatu
ฦณan matan na fargabar cewa damuwar da duniya ta nuna a kansu na raguwa, duk da cewa kullum suna rayuwa cikin takaicin abin da ya faru - lamarin ya ฦara yi musu ciwo a makon nan ganin an shiga sabon zangon karatu ba tare da su.
"Idan na ga maza na tafiya makaranta da kuma yin duk abin da suke so, hakan yana min zafi. Bana jin daษi. Idan na ga ษan uwana na tafiya makaranta, sai na rasa mai yake min dadi,'' in ji Tamana.
Hawaye ne ke zuba a idonta yayin da take magana.
"Tun da farko, ษan'uwana ya sha cewa ba zai tafi makaranta, ba tare da ni ba. Na faษa masa cewa ya yi hakuri ya tafi zan zo daga baya.
"Mutane sun faษa wa iyayena cewa kada su damu, suna da ษa namiji. Ina ma a ce muna da damammaki iri ษaya."




Comments
Post a Comment