Advertisement

Responsive Advertisement

Kamala Harris ta soma rangadi a nahiyar Afirka


 Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris, ta soma rangadi a kasashen Afrika, inda birnin Washington ke kokarin inganta huldarta sakamakon gogayya da take fuskanta daga kasashe irinsu China da Rasha. 

Kamala Harris za ta kai ziyara kasashen Ghana da Zambia da Tanzania domin tattauna batun kasuwanci da tsaro da inganta demokuradiya. 

Tudadar manyan jiga-jigan gwamnatin Amurka sannu a hankali a nahiyar Afirka na sake bayyana karuwar fahimtar da Amurka ke yi kan bukatar inganta alakarta da nahiyar. 

Wannan ya biyo bayan girmaman gogayya da ake samu tsakanin manyan kasashen duniya, musamman China da Rasha da ke shiga jikin 'yan Afirka.

Mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris za ta soma rangadinta na kwanaki tara daga Ghana, sannan ta je Tanzania ta kuma kammala da Zambia.

k

ASALIN HOTON, REUTERS

Bayanan hoto, 

Matar Joe Biden, Jill Biden a ziyarar da ta kawo Afirka a watan Fabarairu

Ghana, da ta mayar da hankali wajen inganta alaka da 'yan Afirka da ke zaune a ketare da kuma inganta matsalolin dimokuradiya, wannan tamkar ya bude kofa da bai wa Ms Harris damar sanin inda za ta karkata.

Wannan rangadi nata, a cewar wata sanarwa da aka fitar, kokari ne na sake karfafa batutuwan da aka cimma a taron Amurka da Kasashen Afirka da aka gudanar a Disamban bara a Washington, inda Shugaba Joe Biden ya jaddada cewa Amurka a yanzu bata da burin da ya zarta inganta makomar Afirka.

Sai dai karuwar matasa da kuma habbakar al'umma da kuma tarin albarkatun da ke nahiyar, su ne ke sake jawo hankali da kwadaita manyan kasashe da ke son ganin an dama da su kuma sun yi tasiri a nahiyar.

Yayinda ziyarar Sakatare Janar Anthony Blinken a kasashen Habasha da Nijar ta mayar da hankali kocokan kan batun tsaro, mataimakiyar shugabar kasa, Kamala Harris za ta mayar da nata hankali ke kan batun matsalolin tattalin arziki da galibin kasashen Afirka ke fama.

Masana dai na ganin burin Amurka shi ne tabbatar da cewa martabarta bata gushe a idon 'yan Afirka ba, musamman a wannan lokacin da manyan kasashe a duniya abokan gasarsu ke rungumar Afirka. 

Ga kuma Rasha da take sake fadada ayyukanta na soji a nahiyar.

Post a Comment

0 Comments