Advertisement

Responsive Advertisement

Waiwaye: Zaɓen gwamnoni da fara azumin Ramadana

 

An yi zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar dokokin jihohi

.

ASALIN HOTON, INEC

A makon da ya gabata - ranar 18 ga watan Maris aka yi zaɓen gwamnoni da ƴan majalisar dokoki na jihohi a jiha 28 na Najeriya.

Zaben ya yi zafi a wasu jihohin ƙasar da har ta kai ga samun taƙaddama kafin a sanar da sakamakon zabensu.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar INEC ta bayyana cewa bayan zaɓen, Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar ta ta lashe jihohi 15, sai PDP da ta samu jihohi 9, NNPP da Labour kuma suka samu jiha ɗaya kowannensu.

Akwai kuma jihohi biyu - Adamawa da Kebbi da INEC ta ce zaɓensu bai kammala ba saboda matsaloli da kuma ƙalubalantar zaɓukan da jam'iyyu suka yi kuma zuwa yanzu hukumar ba ta ayyana ranar da za a sake gudanar da zaɓe a jihohin ba.

Zaɓen dai ya samar da zaɓaɓɓun gwamnoni 17 da za su soma mulki da zarar an rantsar da su a watan Mayu.

Akwai kuma gwamnoni masu ci guda tara da aka sake zaɓa domin yin wa'adi na biyu.

Zaɓen ya bar waɗansu ƴan siyasa cike da murna yayin da wadansu ƴan siyasar suke cike da bakin ciki, saboda yadda sakamakon ya kasance.

A waɗansu jihohin ƙasar an samu sauyi a jam’iyyar da ke mulki inda ƴan adawa suka samu nasara a yayin da a waɗansu kuma masu mulkin ne suka samu dama domin ci gaba da jan ragama.

Post a Comment

0 Comments