Advertisement

Responsive Advertisement

Me ya sa kika azabtar da ni?': Wata ƴar aikin gida da take neman a yi mata adalci


 Ku agaza mun, wacce ta dauke ni aiki tana azabtar da ni.” Meriance Kabu ta rubuta.” Kullum sai an yi mun jina-jina a agaje ni!


Daganan sai ta kanannade takardar ta jeho ta, ta tsakanin karafunan kyauren da aka garkame gidan, wanda yake wajen Kuala Lampur inda take aiki a matsayin `yar aikin gida.


Wata mata da ta zo wucewa ta tsinci takardar a kasa. Tana karanta takardar ta maza ta kai wa wani jami`in `yan sanda mai murabus da shi ma yake zaune a wadannan gidaje. “In da ta ci gaba da zama a wajen, tabbas da ta mutu.,” ya bayyana daga bisani. 


A wannan rana, 20 ga watan Disamba na shekarar 2014, `yan sandan Maleshiya suka je suka buga kyauren kofar inda Mariance take. 


Wajen da ta kasa fita a watanni takwas. “Ji nake kamar ina faduwa” ta bayyana a lokacin da take tuna lokacin da ta ga jami`an. 


“Suka ce, `Kada ki ji tsoro, ga mu mun kawo miki agaji`. A wannan lokaci na sake jin karfi ya zo mun. Na ji ashe zan iya sake numfasawa. Jami`an `yansandan suka kira ni kusa da su, na fada musu gaskiya.”


Wannan labari yana kunshe da bayani dalla-dalla da wasu daga cikin masu karanta shi, za su iya kasancewa cikin damuwa. 


Shekara 9 ke nan, har yanzu Meriance tana neman a mata adalci. Lamarin nata wanda za a iya cewa ya zama na daban, yana nuna hadarin da `yan zuwa neman aiki ko aikatau a wasu wurare masu nisa, da babu bayaninsu a rubuce suke ciki da kuma yadda adalci yake musu wahalar samu har ma da wadanda suka rayu har suke iya ba da labarinsu. 


A shekarar 2015, `yan sanda sun tuhumi wacce ta dauki Mariance aikin gida, Ong Su Ping Serene, da laifin haddasa mata tsananin rauni, da kokarin aikata kisan kai, da safarar bil`Adama da saba wa dokokin shige da fice. 


Ta ce sam atabau ita ba ta aikata laifuffukan da ake tuhumarta ta aikata ba. Meriance ta ba da shaida a kotu, kafin a karshe ta koma gida cikin iyalanta.

Post a Comment

0 Comments