Advertisement

Responsive Advertisement

Messi ka iya tafiya Amurka, inda dukkanin ƙungiyoyi za su haɗa masa albashi


Manchester City ba ta da niyyar sayar da dan wasan tsakiya na Ingila Kalvin Phillips a bazara mai zuwa duk da cewa ba kasafai take sanya dan wasan mai shekara 27 a wasa ba tun da ta saye shi daga Leeds United. 

Sai dai kuma an ce Phillips na shirin barin kungiyar ganin cewa rashin sanya shi a wasa sosai ka iya shafar damarsa ta samun gayyata zuwa tawagar Ingila

Mai yuwuwa Lionel Messi, ya tafi gasar Amurka ta MLS a bazaran nan, inda kowacce daga cikin kungiyoyin gasar 29 za ta rika bayar da karonta wajen biyansa albashi.

PSG na ci gaba da tattaunawa da wakilan dan wasan tsakiya na Chelsea da Faransa N'Golo Kante.

Mai yuwuwa dan wasan gaba na Leeds United Rodrigo, 32, zai yarda a rage masa albashi idan har zai kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar. 

Kwantiragin dan wasan na Sifaniya na yanzu zai kare ne a bazarar 2024.

Dan wasan gaba na Ingila Bukayo Saka, mai shekara 21, zai samu kusan fam miliyan 15 a kaka daya idan ya sanya hannu a sabuwar yarjejeniya da Arsenal. 

Watakila sai Chelsea ta sayar da 'yan wasa a bazarar nan ta samu kudade masu yawa domin kauce wa saba dokokin gasar Premier na kashe kudi a shekara mai zuwa.

Har yanzu Liverpool ba ta fara tattaunawa da tshon dan wasan tsakiya na Ingila ba James Milner duk da cewa Jurgen Klopp na son ci gaba da rike dan wasan zuwa karin wata shekara daya.

Tottenham na cikin kungiyoyin Premier da ke sha’awar matashin dan wasan Brighton da Jamhuriyar Ireland Evan Ferguson, mai shekara 18. 

Shugaban Tottenham Daniel Levy yana son sanin ko Julian Nagelsmann zai karbi aikin Antonio Conte a matsayin kociyan kungiyar. 

Su kuwa ‘yan wasan Bayern Munich sun rabu gida biyu a kan korar kociyan nasu Julian Nagelsmann, dan Jamus. 

Borussia Dortmund na son sayen matashin dan wasan tsakiya na Irelanda ta Arewa Shea Charles mai shekara 19 daga Manchester City. 

Dole sai Barcelona ta dauki 'yan wasa uku zuwa hudu wadanda ba su da wani kwantiragi a kansu wato na kyauta a bazaran nan sannan kuma ta takaita albashin 'yan wasanta.

Post a Comment

0 Comments