Ranar Laraba kenan yayin da watan azumi ya kama, a ƙasar Libya an haska waɗannan fitilu, domin yin maraba da zuwan watan na Ramadan mai alfarma.
Yayin da aka kama azumin, waɗannan musulman na sallar tarawi a masallacin Amr bin As da ke birnin Al-qahirar Masar.
A ranar Litinin da ta gabata al'ummar ƙasar Tunisiya suka gudanar da bikin zagayowar ranar samun 'yancin kai.
Daruruwan 'yan ƙasar ne suka fantsama kan titunan biranen ƙasar domin nuna murnarsu kan wannan rana, mai matuƙar tarihi a gare su.
Wannan matar na daga cikin mutanen da suka gudanar da bikin murnar zagayowar ranar samun 'yancin kan Tunisiya, inda ta caɓa kwalliya da tufafin gargajiya.
Wannan matar ma na daga cikin waɗanda suka gudanar da murnar bikin na ranar Litinin
Sarauniyar Netherlands Queen Maxima ta ziyarci wata kasuwa a Morocco a wani ɓangare na ziyarar da take yi a ƙasar a matsayinta na jakadiyar majalisar Dinkin Duniya.
Nan kuma a Kigali babban birnin ƙasar Rwanda, waɗannan mutanen ke rawa a bikin Commonwealth da aka gudanar
Mutane na ɗiban ruwa a wata rijiya a birnin Dakar na ƙasar Senegal, kwanaki gabanin bikin 'Ranar Ruwa ta Duniya' da Majalisar Dinkin Duniya ke shiryawa da nufin zaburar da mutane kan matsalar ruwa da duniya ke fuskanta
Ranar Juma'a a Mauritania , waɗannan mutanen na shirin shiga masallaci a garin Chinguetti domin gudanar da sallah
0 Comments