Advertisement

Responsive Advertisement

TSAKANIN EL-RUFAI DA IYALAN ABACHA; Kotu ta yi watsi da kwace ikon mallakan filin Otel ɗin Durbar da El-Rufai ya yi daga iyalan Abacha


 Babbar kotu a Kaduna ta yi watsi da kwace takardun shaidar mallakar fili wato C of O na katafaren filin Otel ɗin Durbar wanda mallakin iyalan marigayi janar Sani Abacha da gwamnan Kaduna mai barin gado Nasir El-Rufai ya yi.

A shekarar 2020 ne gwamnatin jihar Kaduna ta rusa kangon otel din tare da soke takardar shaidar mallakar filin wanda ya kai ga takaddama tsakanin gwamnati da iyalan Abacha.

Lauyan dake kare iyalan Abacha, Reuben Atabo, Babban Lauyan Najeriya (SAN) ne, ya shigar da karar El-Rufai da wasu mutane uku a babbar kotun jihar Kaduna.

Ya zargi gwamnati da rusa kadarorin ba bisa ka’ida ba tare da kwace takardar shaidar mallakar fili wato C of O.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Hannatu Balogun ta yanke hukuncin cewa lallai gwamna El-Rufai ba shi da ikon haramta wannan katafaren fili na Durbar ga iyalan marigayi Abacha wanda suna masu mallakin sa na asali. 

Bayan sauraren bangarorin biyu da maishari’a Balogun ta yi ta ce iyalan Abacha ne ke da gaskiya a takaddamar, cewa El-Rufai yayi karambani ne wajen amfani da madafun iko ya yi karfa-karfa a kan wannan katafaren fili.

Idan ba a manta ba tun bayan darewa gwamnatin Kaduna da El-Rufai yayi a 2015, Hukumar raya birane na jihar Kaduna ta rusa kangon ginin Otel ɗin, bayan gwamnati ta sanar da kwace filin. 

A dalilin haka ne iyalan Abacha su ka garzaya kotu domin bin hakkin filin su da suka yi zargin an yi musu karfakarfa ne a kai.

Za a ci gaba da shari’ar ranar 4 ga Yuli.

Post a Comment

0 Comments