Sanata Orji Uzor Kalu, bulaliyar majalisar tarayya ya ce sabon tsarin sauya fasalin takardun naira ba zai kawo cikas ga nasarar Bola Tinubu ba
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce yana kyautata zaton APC za ta ci zaben shugaban kasar na ranar 25 ga watan Fabrairu saboda yawan magoya bayansu a kasar
Kalu ya kuma ce idan da shine ke matsayin Shugaba Muhammadu Buhari zai yi biyayya ga umurnin kotun koli na cigaba da amfani da tsaffin kudi tare da sabbin
Bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Kalu, ya ce sabuwar tsarin sauya fasalin naira da babban bankin kasa,
CBN, ya fito da shi ba zai shafi yiwuwar samun nasarar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Ahmed Tinubu ba a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.
Ya ce Tinubu ne shugaban kasar Najeriya na gaba kuma babban kwamandan dakarun Jamhuriyyar Tarayyar Najeriya, Daily Trust ta rahoto.
0 Comments