Advertisement

Responsive Advertisement

2023: Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan Ya Yi Sabon Jawabi Ana Kwana 4 Zabe


 Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi kira ga yan Najeriya su zama masu yarda da kaddara a yayin da ake tunkarar zabe Jonathan ya kuma yi kira ga yan siyasa da su guji furta kalaman da za su tada rikici su kuma kyalle dimokradiyyar Najeriya ta girma 

Tsohon shugaban kasar ya kuma yi kira ga matasa kada su yarda yan siyasa su yi amfani da su don cimma burinsu saboda mako ne da za su zabi wanda zai jagorance su

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi sabon jawabi gabanin zaben ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu na shugaban kasa da majalisar tarayya. 

Tsohon shugaban kasar ya yi kira ga zaman lafiya a yayin da ya yi kira ga yan Najeriya masu kishin kasa su kasance cikin lumana tare da rungumar kaddara, Tribune ta rahoto. 

Jonathan ya yi magana kan zaben 2023 Jonathan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ofishinsa ta fitar a ranar Talata, 21 ga watan Fabrairu inda ya yi kira ga yan siyasa su yi watsi da kiyayya da rikici kuma su zama masu dattaku da zurfin tunani yayin yin harkokinsuu gabanin zaben don Najeriya ta tsira. 

Abin da ke faruwa a baya-bayan nan kan tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, Kudu maso gabas, zaben 2023

 Da ya ke kira ga matasa, Jonathan ya ce: "Kasar ta ku ne a nan gaba; kada ku bari a yi amfani da ku wurin lalata kasa da tada rikici. 

Kune za ku gina Najeriya. Wannan zaben ya baku damar ku taka muhimmin rawa wurin zaben shugabannin da ku ke ra'ayi; wadanda za ku iya tambayar su idan basu cika alkawari ba, wadanda ku ka aminta za su kare muku kasarsu su tabbatar da hadin kai da zaman lafiya da cigaban kasar mu." 

Post a Comment

0 Comments