Advertisement

Responsive Advertisement

6 Zabe, ‘Dan Takaran Jam’iyyar NNPP Ya Rasu A Kano


Jam’iyyar adawa ta NNPP ta rasa Kamilu Ado Wudil wanda yake cikin ‘yan takaran zaben 2023 

Majiyoyi da-dama sun tabbatar da rasuwar ‘dan takaran ana saura kasa da mako daya a shirya zabe 

Hon. Kamilu Ado Wudil shi ne yake harin kujerar ‘dan majalisar tarayya na Wudil/Garko NNPP

 Kano - Rahotanni sun tabbatar da rasuwar Kamilu Ado Wudil wanda yake neman zama ‘dan majalisar tarayya a zabe mai zuwan nan.

 Leadership ta ce Hon. Kamilu Ado Wudil mai neman kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya na mazabar Wudil da Garko ya bar Duniya. 

‘Dan siyasar ya rasu ne a Kano a lokacin da ake shirye-shiryen zaben shugaban kasa da kuma ‘yan majalisar tarayya a duk jihohin Najeriya. 

Kamilu Wudil ne yake rike da tutar jam’iyyar NNPP a takarar ‘dan majalisar Wudil da Garko, yana harin lashe zabe a makon nan da aka shiga.

Mutuwar ta zo ne a lokacin da kwanaki shida suka rage hukumar INEC ta gudanar da babban zabe. 

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

 Rahoton ya bayyana cewa Marigayin ya rike shugaban karamar hukumar Wudil a lokacin da Rabiu Musa Kwankwaso yana Gwamna a 1999.

Hon. Wudil ya yi shekaru uku a matsayin shugaban karamar hukumarsa har zuwa shekarar 2002.

 Darektan kafofin sadarwa na zamani na kwamitin yakin zaben NNPP a jihar Kano, Salisu Yahaya Hotoro ya yi maganar wannan rasuwa a jiya. 

A game da mutuwar jami'in na NSCDC, a Facebook aka ji Malam Hotoro yana cewa: "Rai bakon Duniya, Allah ka gafartawa ACG Kamilu Ado Isah.

: Abdullahi Ibrahim daya daga cikin masu tallata siyasar Kwankwasiyya a dandalin sada zumunta ya tabbatar da wannan labari mai ban takaici.

Post a Comment

0 Comments