Advertisement

Responsive Advertisement

'A shafin Facebook na ga gawar mahaifina'


 Lokacin da wani dalibi ɗan ƙasar Habasha Moti Dereje ya shiga shafinsa na Facebook a ƙarshen watan Nuwambar 2018, ya yi tsammanin ganin irin abubuwan da ya saba gani daga abokai da 'yan uwa.

Maimakon haka matashin ɗan shekara 19 da ke karatu a Addis Ababa babban birnin ƙasar sai ya ci karo da abin da ya rikita rayuwarsa.

"Ina shiga domin ganin labarai, sai naga gawar mahaifina a yashe a ƙasa," haka matashin ya shaida wa BBC.

Ba Moti ne kadai ya kaɗu da ganin wannan mummunan hoto ba, amma dai a haka ya gano cewa an kashe mahaifinsa.

"Ƙame wa na yi a lokacin. Abin ya girgiza ni matuƙa,'' ya ƙara da cewa.


Yayin da Habasha ke fama da rikicin siyasa tsawon shekaru, kafafen sada zumuntar ƙasar cike suke da munanan hotuna da hotunan bidiyo, labaran ƙarya da kuma na tunzura mutane da ke tayar da rikici.

Masu fafutuka sun daɗe suna kiraye-kirayen a riƙa tace abubuwan da ake wallafawa a kafafen kafin su janyo wani rikicin.

Shi kuwa Moti maimakon ya ga an cire hoton mahaifin nasa, sai ma ƙara ganin hotuna irin waɗan nan da yake yi.

Mahaifinsa wanda tsohon ɗan majalisa ne, kuma yana aiki da jami'a, yana daga cikin 'yan siyasar da ake neman kashewa a yankin Oromia.

Yankin ya rika fuskantar tashe-tashen hankali, a lokacin da ake yawan samun kashe fitattun mutane.

"Kamar ma farin cikin kashe shi suke yi. Abu ne mai matukar raɗaɗi," in ji Moti.

BBC ta ga waɗan nan hotuna guda 15, wanda Moti ya ce ya kai kokensa ga Facebook domin su cire su.

Hukumomin Faceboook sun yi alƙawarin cewa idan iyalai a ƙasar suka shigar da ƙorafi kan hoto mai tattare da tashin hankali za su cire shi.

Sai dai Moti ya shigar da koken bai san adadi ba cikin shekara hudu kuma har yanzu ba a cire ba.


Post a Comment

0 Comments