Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ke neman takarar shugabancin Najeriya shekara takwas baya, ya zo da alƙawarin cewa zai taimaka wajen kawo karshen matsalar Boko Haram wanda ya tilastawa Miliyoyin mutane barin muhallansu daga arewa maso gabashin ƙasar zuwa wasu yankuna.
Yanzu shekara takwas kenan da wannan alƙawarin kuma yanzu ya samu zaman lafiya, kuma an kwato wasu yankuna masu girma wanda a baya mayaƙan Boko Haram suka ce sun ƙwace su. Sai dai yayin da 'yan Najeriya ke ƙoƙarin zaɓar magajinsa, halin da ake ciki cike yake da ru ɗani.
Ruƙayya Goni wadda ke zaune kusa da wata makarantar firaimare da masu iƙirarin jihadin suka ƙona, lokacin da suka ƙwace yankin Damasak a ƙarshen 2014.
Manufar Boko Haram dai ita ce "ilimin boko haramun ne" kungiyar ta sha kai hare-harenta kan makarantun da babu ruwansu da addini, tare da sace sama da 'yan makaranta 200 daga garin Chibok.
Shekara tara da ta gabata, Ruƙayya ta gudu daga gidanta tare da iyalanta su 11, inda suka tsallaka iyakar da take kusa da su ta ƙasar Nijar.
"Mun gudu ne saboda matsalar tsaro da Boko Haram ta janyo" ta bayyana da yaren Kanuri, kuma wani mai fassara ya fassara. "Sun kwace Damasak shi yasa muka tsallaka Diffa, da ke Nijar." A lokacin tana da 'yarta 'yar shekara shida da haihuwa. Ta haifi duka 'ya'yanta maza biyar a Nijar daga baya kuma ta koma Damasak a bara.
"Mun ji cewa komai ya daidaita a yanzu, shi yasa muka yanke shawarar mu koma gida," kamar yadda ta yi bayani. Na tambayeta ko ta taɓa tunanin komowa gida. "Eh muna ta fatan komawa gida, kullum sai mun yi addu'ar zaman lafiya. Na ji daɗin koma. Babu wani wuri da ya fi gida.
0 Comments