Advertisement

Responsive Advertisement

Canjin Kudi Ya Jawo Karuwai Su na Kuka, Ana Samun karancin Abokan Yin Lalata

 


Wasu daga cikin matan da suke zaman kan su a garin Abuja ba su ji dadin canza takardun kudi ba

 Da aka zanta da matan sun nuna cewa ana samun kalubale wajen tura masa kudi a asusun bankinsu 

A dalilin karancin kudi a hannun jama’a, wasu kan yi rangwamen dole idan mutum na da kudi DUBA NAN: Danna “See First” karkashin karkashin "Following “ don samun labarai a shafinka na Facebook akai-akai 

Abuja - Mata masu zaman kan su a babban birnin tarayya Abuja, sun nuna yadda suke fama da rashin ciniki a dalilin canza manyan kudi da aka yi.

 Hukumar dillacin labarai na kasa ta zanta da wasu daga cikin wadannan mata da suke zaman kan su, domin jin yadda suke neman kudi a halin yanzu. 

Matan sun bayyana cewa karancin takardun kudi ya jefa kasuwancinsu a wani halin ha’ula’i, su na ganin tsarin da aka zo da shi barazana ne a gare su. 

Duk da alheran da suke gani tattare da sauya kudin da aka yi, matan sun nuna abin ya taba su. 

"Yanzu ba a samu sosai a harkar domin a yau babu takardun kudi a ko ina. Idan an yi ciniki, wasu abokan harkar sai su tambayi lambar akawun dinka. 

Sai dai su ce za su aika maka kudi ta akawun, idan na bada lambar asusun, sai su latsa wayarsu, sai su fada mani cewa ai sun aiko mani da kudina. 

Post a Comment

0 Comments