Advertisement

Responsive Advertisement

Ana Gobe Zabe, An Kama Wani Mutum Da Maƙuden Miliyoyin Naira A Mota Zai Kai Wa Ɗan Siyasa A Gombe


 An kama wani mutum dauke da takardun naira cikin jaka ta 'Ghana must go' a mota a jihar Bauchi 

Mutumin mai suna Hassan Ahmed ya bayyana cewa zai kai wa wani dan siyasa ne kudin a jihar Gombe 

Mai magana da yawun hukumar ICPC a Bauchi, Ogugu, ya ce suna yi wa wanda ake zargin tambayoyi don zurfafa bincike 

Jihar Bauchi - Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta kama wani Hassan Ahmed dauke da tsabar kudi naira miliyan 2 na sabbi da tsaffin naira a yayin da ake fama da karancin kudi a kasar, rahoton The Punch. 

Dakarun 33 Artillery Brigade da aka tura Alkaleri a jihar Bauchi ne suka kama shi a ranar Juma'a 24 ga watan Fabrairu suka mika shi ga ofishin hukumar yaki da rashawar a Bauchi. 

Kakakin ICPC, Azuka Ogugua, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a daren ranar Juma'a. 

Ogugua ya ce:

 "Ahmad na dauke da tsabar kudi N900,000 na sabbin naira da N1.1 miliyan na tsaffin naira kuma yana dauke da kudin ne cikin wata mota kirar Hilux mai bakin launi mai lamba JMA 85 AZ. 

"Kudin da aka saka su cikin jaka ta 'Ghana Must Go, sun hada da kunshin N1,000 na N600,000, kunshi shida na sabbin N500 na N300,000, da tsaffin naira dari biyu na N1.1 miliyan.

" Ogugua ya kara da cewa hukumar ta riga ta fara bincike, a yayin da wanda ake zargin ya bayyana cewa yana hanyar kai wa wani dan siyasa ne kudin a Jihar Gombe. 

Post a Comment

0 Comments