Advertisement

Responsive Advertisement

Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwar Maiduguri Ta jihar Borno


 Mummunar gobara ta tashi a shahararriyar kasuwar nan ta 'Monday Market' da ke garin Maiduguri a jihar Borno 

Dubban shaguna sun kone kurmus a gobarar inda aka yi asarar dukiya ta miliyoyin naira 

Hukumar kashe gobara ta kwana-kwana na nan tana kokarin kashe wutar wacce ba a san musababbin tashinta ba

Borno - Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa gobara ta tashi a babbar kasuwa ta 'Monday Market' da ke jihar Borno. 

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gobarar ta fara da misalin karfe 2:00 na tsakar daren ranar Lahadi, 26 ga watan Fabrairu kuma ta yadu zuwa bangarori daban-daban na kasuwar.

Post a Comment

0 Comments