Advertisement

Responsive Advertisement

Jam'iyyar ADC Ta Janye Daga Neman Shugaban Kasa, Ta Koma Bayan Peter Obi


 Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya samu gagarumin karin goyon baya ana dab da zabe 

Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa bayan dogon nazari ta yanke shawarar marawa Obi baya ya zama magajin

 Buhari Nan da kwana ki 5 watau ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, 2023 za'a gudanar da zaben shugaban ƙasa da na majalisun tarayya 

Abuja - African Democratic Congress (ADC) ta bayyana goyon bayanta ga ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party, Peter Obi gabanin zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023.

 Jam'iyyar ADC ta sanar da wannan matakin da ta ɗauka yayin taron yan jarida a birnin tarayya Abuja ranar Litinin, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron manema labaran sun haɗa da shugaban ADC na ƙasa, Raphael Nwosu, da kuma babban jigon Labour Party (LP) kuma na hannun daman Obi, Pat Utomi. 

Rahotanni sun nuna cewa Peter Obi da abokin takararsa, Datti Baba Ahmed, ba su samu halartar wurin ba saboda suna Zariya, jihar Kaduna, inda suka je Ralin kamfe.

Post a Comment

0 Comments