Ana dab da zaben shugaban ƙasa, jam'iyyar PDP ta kori ɗan takarar gwamnan Akwa Ibom a zaben watan
Maris mai zuwa Tun bayan kammala zaben fidda gwani a shekarar 2022 ake tirka-tirka kan tikitin takarar gwamnan jihar
A ranar Jumu'a da ta shige aka ga INEC ta sauya ɗan takarar PDP a Akwa Ibom bayan umarnin Kotu
Akwa Ibom - Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Akwa Ibom ta fatattaki Michael Enyong, ɗan takarar gwamnan jihar a zaben da ke tafe.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa PDP mai mulkin jihar ta ɗauki wannan mataki ne kan zargin da ake masa na amfani da takardun Bogi.
Hakan na ƙunshe a wata wasika mai kwanan watan 30 ga watan Janairu kuma ɗauke da sa hannun shugaban PDP na ƙaramar hukumar Uyo, Anthony Eko, da mambobin majalisar zartaswa 14.
Wasikar na ɗauke da adireshin shugaban PDP na jihar Akwa Ibom. Wanda abun ya shafa, Mista Enyong, mamban majalisar wakilan tarayya mai ci, ya fito ne daga Uyo.
0 Comments