Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban jam'iyyar PDP na gunduma a karamar hukumar
Giwa da ke jihar Kaduna Wani ganau ya bayyana cewa maharan sun saje da jirgin yakin neman zabe da ya shiga kauyen kuma wannan ne karo na farko
Bayan ษan siyasan, yan bindigan sun sace wani shugaban al'umma jim kaษan bayan sun dawo daga wurin kamfe
Kaduna - Wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban Peoples Democratic Party (PDP) da shugaban al'umma a ฦaramar hukumar Giwa, jihar Kaduna.
Wani Ganau ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa yan bindigan jejin sun kutsa cikin ฦauyen ฦan Mahawayi da misalin karfe 11:00 na daren ranar Lahadi kana suka yi gaba da mutanen biyu.
Waษanda suka faษa hannun yan ta'addan su ne, Alhaji Bala Alhassan Marafa, shugaban jam'iyyar PDP na gundumar Dan Mahawayi da kuma Suleiman Isiyaku Mai Siga.
"Baki ษayanmu mun ษauka yan bindiga na daga cikin tawagar kamfen da ta shigo yankin saboda bayan mutanen biyu sun dawo daga wurin taron kamfe ne yan ta'addan suka tasa ฦeyarsu."
"Wannan shi ne karo na farko da aka yi garkuwa da wani a kauyen ฦan Mahawayi.
" Haka nan wani ษan Banga ya ce lamarin ya faru ne bayan gama ralin kamfen ษan takarar majalisar tarayya mai wakiltar Giwa da Birnin Gwari, Aminiya ta rahoto.
Mazauna garin ฦan Mahawayi sun jaddada cewa wannan ne hari na farko da yan bindiga suka kai masu domin suna zuwa biyan bukatunsu amma ba su kai hari
Duk wani yunkuri na jin ta bakin shugaban jam'iyyar PDP na ฦaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna, ya ci tura har zuwa lokacin haษa wannan rahoto.

Comments
Post a Comment