Advertisement

Responsive Advertisement

KAI TSAYE: Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Sun Fara Shigowa


 Sakamakon zabe sun fara fitowa daga runfunan zabe da dama a fadin tarayya. 

An rufe tantance masu niyyar zabe a karfe 2:30 na rana bisa tsarin INEC. 

Ku biyo nan don samun sakamako da duminsu daga runfunan zabe.

Shugaban APC na Kano ya sha kaye a mazabarsa Shugaban jam'iyyar APC ta jihar Kano, 

Abdullahi Abbas, ya sha kaye hannun Kwankwaso a mazabarsa da ke karamar hukumar Gwale. 

PU 33, Balarabe Haladu Community School, Chiranchi, Gwale LGA. 

APC: 70 

NNPP: 106 

Atiku Ya Lallasa Tinubu a rumfar zaben shugaban majalisa Ahmad Lawan 

Dan takarar shugaban kasan APC, Tinubu, ya sha kashi a akwatin shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan. 

Ga sakamakon zaben shugaban kasa: Katuzu Primary School PU 001B., Gashua 

APC - 107 

PDP - 186 

NNPP - 41 

LP - 1

Sakamakon zaben Gwagwalada Custom Command, Abuja 

LP 210 

APC 30 

PDP 14 

Kwankwaso ya lashe rumfar sarkin Kano 

Sanata Rabiu Kwankwaso ya lashe rumfar zaben sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, da ke Kofar Kwaru. 

NNPP - 99 

APC - 39 

PDP 32 

LP – 1 

APGA - 2 


Post a Comment

0 Comments