Talata, 21 ga watan Fabrairu ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), zai gudanar da gangamin kamfen dinsa na karshe a filin wasa na Teslim Balogun Stadium (TBS) da ke jihar Lagas.
Tun bayan da ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na APC, Tinubu ya gudanar da gangamin kamfen guda biyu a jihar da ya mulka a matsayin gwamna.
Kai Tsaye: Yadda Gangamin Kamfen Din Tinubu/Shettima Ke Gudana A Lagas Asali: Original Ana sanya ran Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai jagoranci dukkanin gwamnonin jam'iyyar mai mulki da sauran masu ruwa da tsaki zuwa
TBS gabannin babban zaben na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.
Wasu masu lura da harkokin siyasa suna ganin cewa wannan gangamin na da matukar muhimmanci ga Tinubu saboda dole ya dakushe manyan abokan hamayyarsa,
Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party wadanda suka gudanar da manyan gangami a Lagas.
Zan yi wa Najeriya aiki tukuru kamar yadda Buhari ya yi mani, Tinubu a gangamin kamfen dinsa na karshe
An yi wa Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC kara sosai a wajen gangamin kamfen dinsa na karshe wanda ya gudana a Lagas.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya halarci gangamin ya sake daga hannun Tinubu a matsayin shugaban kasar gobe da izinin Allah.
Da yake jawabi a wajen kamfen din, Tinubu wanda ke fuskantar shugaban kasar ya ce: "Kamar yadda ka yi mun aiki tukuru, zan yi wa Najeriya aiki tukuru.
Za mu bi duk wasu tsare-tsare da muka tanada a manufofinmu don sabonta muradan yan Najeriya."
Tinubu ya yi godiya ga shugaba Buhari kan tsayin daka da ya yi wajen tabbatar da damokradiyya, gaskiya da kuma adalci.
"Shugaban kasar ya bukaci dukkaninmu da muke da ra'ayi mu je mu yi takara a zaben fidda gwanin jam'iyyarmu inda daleget suka zabe ni, bai bukaci su sauya sakamakon zaben ba sanoda kabila ko addini ko saboda ni ba dan Daura bane kamar shi, ya amince da ni sannan ya tayani murna, yana mai cewa mun 'ka kusa kaiwa wajen'.
" Dan takarar na APC ya ce ya zabi Sanata Kashim Shettima wanda ya bayyana a matsayin mai ilimi da sanin ya kamata a matsayin abokin takararsa.
Ya ce Shettima ya nuna jajircewa wajen gudanar da ayyukansa kuma ya bambanta, yana mai bayyana shi a matsayin mutum abun dogaro, mai amana kuma jajirtacce.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya yi godiya ga mutanen jihar kan yadda suka fito kwansu da kwarkwatansu don tarban shugaban kasa Buhari da Asiwaju Tinubu sannan suka kuma halarci gangamin kamfen din.
Ya ce wannan fitowar da jama’a suka yi ya nuna soyayyar da suke yiwa dan birnin, inda ya bukace su da su fito a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu domin zabar Asiwaju a matsayin shugaban kasa.
Wadanda suka yi jawabi a gangamin sun hada da shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Tinubu Shettima kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da uwargidar dan takarar shugaban kasar na APC, Sanata Oluremi Tinubu.
Ba na adawa da takarar Tinubu, ina tare da shi dari bisa dari, Buhari Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada goyon bayansa ga Tinubu a zaben shugaban kasa.
Buhari ya ce baya adawa da dan takarar na APC kuma yana tare da shi dari bisa dari. Ya kuma ce shine zai lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu inda ya ce daga ranar Litinin zai koma shugaban kasa mai jiran gado.
"Ba na adawa da Asiwaju Tinubu ni nashi ne dari bisa dari…Zuwa Litinin za a kira shi da zababen shugaban kasa mai jiran gado na tarayyar Najeriya.”
0 Comments